
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa da gangan wasu ‘yan Najeriyar ke karawa kayan da suke sayarwa farashi dan kawai su batawa gwamnatinsa suna.
Hadimin shugaban kasar me bashi shawara akan tattalin arziki, Tope Fasua ne ya bayyana hakan.
Yace banda alkaluma tattalin arziki, akwai sauran abubuwan da ke sanya farashin kayan masarufi su tashi a Najeriya, hadda muguntar wasu ‘yan kasar.
Ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook yayin da yake martani ga wani rahoto dake cewa wani gidan mai yana biyan ma’aikatansa Naira Dubu 10.