
Hukumar kula da hakkin mallaka ta Najeriya ta gargadi DJ masu saka wakoki a gidajen biki dasu nemi lasisi ko izinin masu wakokin da suke sakawa.
Hukumar tace rashin bin wannan doka na dauke da hukuncin biyan tarar Naira Miliyan daya ko zaman gidan yari na shekara 5.
A kasashe irin su Amurka dai ba DJ ne ke biyan lasisi ba, me hidimar biki ko me gidan taron ko me Club ne zai biya wannan tara.