
Mutum bakwai ne suka rasu sakamakon kifewar kwalekwale a yankin ƙaramar hukumar Shagari da ke jihar Sokoto a arewacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a lokacin da matafiyan suka fito daga Gidan Hussaini zuwa ƙauyen Gwargawu a ranar Litinin da misalin ƙarfe 9:30 na safiya, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta ƙasa Nema ta bayyana.
Nema ta ce bayanai sun nuna iska mai ƙarfi ce ta haddasa kifewar jirgin ruwan.
A watan Oktoban 2024 ma wani jirgi ya kife da kusan mutum 300 a yankin Mokwa na jihar Neja da ke tsakiyar Najeriyar. Kafin haka, mutum 24 ne suka mutu a kifewar wani jirgin a watan Satumban 2023 a jihar.