
Babban Fasto a jihar Kaduna, Reverend Timothy Yahaya ya caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda ya bayyana cewa, yayi wuri a fara yakin neman zaben.
Yace yana kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya dakatar da yakin neman zaben inda yace sai kwanaki 90 kamin zaben ya kamata a fara yakin neman zaben.
Reverend Timothy Yahaya yace gaba daya an manta da yiwa mutane aiki inda aka koma yakin neman zabe wanda a baya ba haka tsarin yake ba a kasarnan.