
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya bayyana cewa, karya ake masa shi baice an kaiwa tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai hari ba.
Rahotanni sun watsu cewa, Sanata Ali Ndume ya ce an kaiwa Buratai hari a ranar Juma’ar data gabata inda ya tsallake rijiya da baya.
Saidai a bayanin Sanata Ali Ndume bayan da wancan labari ya watsu shine shi bai ce haka ba, cewa yayi an kaiwa garin Buratai hari ne ba tsohon shugaban sojojin ba.
Mayakan kungiyar dake ikirarin Jìhàdì ta Bòkò Hàràm dai sun dawo gadan-gadan inda suke kaiwa jami’an tsaro hare-hare akai-akai inda wasu rahotannin ke cewa ma sun fi sojojin Najeriya makaman yaki.