Friday, December 5
Shadow

Ka Daina Boye-Boye Ka Fito Fili Ka Koma Jam’iyyar APC, Matawalle Ga Gwamnan Zamfara

Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya, kuma tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Bello Mohammed Matawalle, ya bukaci Gwamna mai ci, Dr. Dauda Lawal, da ya fito fili ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar APC ya daina wani boye-boye.

Da yake jawabi a gidansa da ke Maradun yayin wata ziyarar gaisuwar Sallah da dubban magoya baya suka kai masa, Matawalle ya ce lokaci ya yi da Gwamna Lawal zai daina “kumbiya-kumbiya” yana rufa-rufa” ya fito fili ya bayyana matsayarsa a jam’iyyance.

“Kofar jam’iyyarmu a bude take ga duk wanda ke neman ci gaban gaskiya ga jihar Zamfara da Nijeriya,” inji Matawalle, yana mai jaddada cewa bai dauki komai a ransa ba dangane da zabin siyasar Gwamna Lawal.

Ya ce APC jam’iyya ce da ke kan turbar tawali’u, gaskiya da shugabanci nagari.

Karanta Wannan  Hujjojin da kuka kawo na banza da wofi ne, A kul kuka kaiwa Najeriya Khari>>Kasar China ta gargadi Amurka

“Muna kira gare shi ya shigo jam’iyyar a fili da gaskiya, ba ta bayan gida ba,” ya kara da cewa.

Matawalle ya zargi Gwamna Lawal da amfani da “dabarun siyasa da yaudara” tare da kira gare shi da ya rungumi zaman lafiya, cigaba da gaskiya a mulki.

A wani mataki na nuna sadaukarwa ga matakin tushe, Matawalle ya gudanar da wani taron dabarun siyasa da manyan jiga-jigan jam’iyya daga kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara.

A wajen taron, ya raba Naira miliyan 140 da kansa — miliyan 10 ga kowace karamar hukuma — domin karfafa jam’iyyar APC daga tushe a fadin jihar.

Ya bayyana cewa an bayar da kudaden ba tare da wani sharadi ba, yana mai cewa burinsa shi ne karfafa al’umma da hadin kai.

Karanta Wannan  Wada Mutuniyar Maiwushirya tace taga an daina mata like da comment da share a videos din da take yi, dan haka tana neman a dawo a ci gaba da yi dan darajar Annabi(sallallahu Alaihi Wasallam)

Ministan ya yaba wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai kiransa “shugaban zaman lafiya da cigaba” wanda ke da hasashen ci gaban kasa.

Ya bukaci al’ummar jihar Zamfara su mara wa shirin Renewed Hope na shugaban kasa baya, musamman a fannonin tsaro, noma, ilimi da tattalin arziki.

Matawalle ya bayyana wasu nasarori da gwamnatin Tinubu ta samu wajen yaki da rashin tsaro, ciki har da hallaka manyan shugabannin ‘yan bindiga da ci gaba da ayyukan soji a Arewa.

Ya ce ma’aikatar tsaro na da yakinin dawo da cikakken zaman lafiya a jihar Zamfara kafin karshen shekarar nan.

Sai dai ya soki gwamnatin Gwamna Lawal bisa abin da ya bayyana a matsayin rashin tabbatattun sakamako a yaki da ‘yan bindiga.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda shugaban jarabawar JAMB ya fashe da kuka saboda kuskuren hukumar yasa dalibai da yawa sun fadi jarabawar

Ya zargi gwamnatin Lawal da yaudarar jama’a da gazawa wajen cika alkawuran tsaro.

Matawalle ya kwatanta zamansa da wanda ke yanzu, yana cewa lokacin da yake mulki yana samun Naira biliyan 3 zuwa 4 ne a kowane wata, yayin da Lawal ke karbar tsakanin biliyan 19 zuwa 24 a wata.

Ya kalubalanci gwamnan da ya fito fili ya bayyana adadin kudin da yake karba da kuma yadda ake kashe su a fili.

A karshe, Matawalle ya sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar APC da kuma jajircewarsa ga jin dadin al’ummar Jihar Zamfara.

Ya yi kira da a ci gaba da hada kai, shugabanci na gaskiya da goyon bayan jama’a ga manufofin gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *