
Rahotanni daga jihar Kogi na cewa, wani tsohon soja me suna Major Joe Ajayi ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane duk da danginsa sun biya kudin fansarsa Naira Miliyan 10.
An yi garkuwa dashine a gidansa dake Odo-Ape na karamar hukumar Kabba-Bunu ranar May 21, 2025 da misalin karfe 11:30pm.
Da farko dai wanda suka yi garkuwa dashi sun nemi Naira Miliyan 50 inda daga baya da suka ga bashi da lafiya zai rasu.
Sai suka ce a kai musu Naira Miliyan 10, bayan da aka kai musu, suka bayyana inda za’a je a daukeshi, sai gawarsa aka tarar.
Tuni aka kai gawar tasa zuwa mutuware dake Asibitin Kabba Specialist Hospital.
Masu garkuwa da mutane sun matsawa jihar Kogi a ‘yan kwanakinnan.