Friday, December 5
Shadow

Ji yanda Bòm ya kàshè masu yawon murnar sallah a Sakkwato

Kimanin mutum bakwai sun riga mu gidan gaskiya bayan tarwatsewar wani abun fashewa da ake zargi mayaƙan Lakurawa sun dasa a Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato.

Aminiya ta ruwaito cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su da ke kan babura na hanyarsu ta dawowa daga yawon bikin sallah a ƙauyen Gwabro.

Bayanai sun ce an dasa abun fashewar ne a ƙarƙashin wata itaciya da ke zaman wurin hutawar dakarun sojoji a lokacin da suka fito sintiri a yankin.

Majiyiyo sun ce mutum shida sun mutu nan take yayin da ɗaya daga cikin wasu mata biyu yara da suka jikkata ta rasu washegari.

Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Tangaza, Alhaji Ghazzali Rakah ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa waɗanda abin ya shafa mazauna ƙauyen Zurmuku ne.

Karanta Wannan  Ba zaka bata mana suna ba, Ka kawo shaidar cewa, Sai an biya Naira Miliyan 3 ake gabatar da kudirin doka a majalisa ko mu hukunta ka>>Majalisar Wakilai ga dan majalisa, Ibrahim Usman Auyo

Wannan dai ba shi na farau ba, domin kuwa a watannin da suka gabata sojoji da dama sun rasu sakamakon tashin abin fashewa a karamar hukumar.

Har yanzu dai matsalar tsaro babbar damuwa ce a wasu sassan Jihar Sakkwato, inda mazauna ke ci gaba da kiran mahukunta da su ƙara jajircewa wajen daƙile ta’adar masu tayar da ƙayar baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *