Friday, December 5
Shadow

Tinubu ne ke daukar nauyin rikicin dake faruwa a jam’iyyar mu ta Labour party>>Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ke da alhakin rikicin dake faruwa a cikin jam’iyyar su.

Obi ya bayyana hakane a yayin da ake masa tambayoyi a gidan Talabijin na Arise TV inda yace yana da tabbacin Gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyin rikicin dake faruwa a jam’iyyar.

Ya bayyana cewa, suna son yada rikici a cikin jam’iyyar ta Labour Party.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Rashida Mai Sa'a ta jawo cece-kuce bayan data kawo wani Kwado wanda tace na matan aure ne da mazansu ke bin mata a waje, tace kwadon yana hana Zarmalulun Namiji tashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *