
Wani matashi na shan Tofin Allah tsine bayan da yayi wani Bidiyo yana tsinewa mahaifiyarsa inda yace ta haifishi yana shan wahala abinci ma da kyar yake samu.
Da yawa sun tsine masa inda suka rika tunawa mutane da su rika yin addu’ar Kwanciya da iyali dan ana tunanin hakan zai sa ba za’a rika haifo irinsa ba.
Saidai matashin ya bayyana cewa dan neman suna yayi kuma da talauci, inda yace iyayensa mutanen kirki ne kuma baya son a zagesu.
Wasu dai sun bayar da shawarar a kai yaron gidan mahaukata dan da alamar yana da tabin hankali.