
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, an jefi sarki Muhammad Sanusi II a yayin hawan fanisau.
Bidiyo ya karade kafafen sada zumunta inda aka ji wasu na fadar cewa an jefi sarkin.
Dubban masoya ne dai suka raka Sarki Sanusi Hawan Fanisau inda a wata majiyar ake cewa sun kai mutane Miliyan 5.