Friday, December 5
Shadow

Alummar garin Mokwa na fargabar ɓarkewar cùtùkà saboda gàwàrwàkìn da ba a gano ba

Aƙalla makonni biyu da afkuwar ambaliyar ruwan da ta hallaka mutane tare da share gidaje masu dimbin yawa a garin Mokwa na jihar Neja, jama’ar yankin na kokawa kan yadda aka soma jin warin gawarwakin mutanen da har kawo yanzu ba a kai ga ganowa ba.

Jama’a dai na ci gaba da bayyana cewa warin na iya haifar da matsala ga lafiya, musamman ana fargabar barkewar kwalara kasancewar da dama daga rijiyoyin jama’a da suke samun ruwan sha sun rufta.

Daga cikin wadanda BBC ta zanta da su, sun ce tun daga ranar asabar ta karshen makon daya gabata suka soma jin warin gawarwakin.

Karanta Wannan  Sadiya Haruna ta kara aure, ji bayani dalla-dalla kan wa ta aura, shin ta ma yi idda, sannan a ina aka daura auren?

Sai dai wasu mazauna garin na Mokwa sun ce a yanzu dai fargabar da ake da ita ta ɗan ragu bayan da aka soma yin feshin magani a wasu wurare.

Sun kuma ce Unicef ta bayar da wasu magunguna da ake sawa cikin ruwan da za ayi amfani da shi masu kashe ƙwayoyin cutuka.

Daraktan hulda da jama’a na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa reshen jihar Niger, Dakta Ibrahim Hussaini Audu ya ce tun daga soma samun warin gawarwakin da ba a kai ga ganowa ba har yanzu, gwamnatin jihar ta dauki matakan gaggawa na raba mutane da wurare, da kuma kai musu tsaftattacen ruwa domin sha.

Karanta Wannan  Masu Laifi 16 sun tsere daga gidan gyara hali dake Keffi jihar Nasarawa

Tun bayan aukuwar ambaliyar ruwan ta Mokwa da ta yi matuƙar muni, hukumomi a jihar ta Niger sun ce adadin mutanen da suka mutu sun haura 230, yayin da har yanzu ba gano sama da mutum 400 ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *