Friday, December 5
Shadow

Tsohon Tsageran Naija Delta, Tampolo yawa shugaban kasa, Tinubu alkawarin kuri’u Miliyan 10 a zaben 2027

Wata kungiya karkashin tsohon tsageran Naija Delta, Tampolo ta yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin kuri’u dubu 10 a zaben 2027.

Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar me suna Comrade Sunday Adekanbi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar ‘yancin Najeriya a Abuja inda ya jawo hankalin ‘yan Najeriya da su shiga kungiyar.

Yace a shekaru 2 da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi yana Mulki, ya dora Najeriya a Turbar ci gaban tattalin arziki.

Yace zasu yi aiki bisa jagorancin Tampolo dan tattaro kan ‘yan Najeriya su goyi bayan gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027.

Karanta Wannan  An kama sojojin da aka aika su tsare makarantar 'yan mata ta jihar Kebbi amma suna koma daukar hoto da 'yan matan sannan suka tafi yawo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *