Friday, December 5
Shadow

Yawan man fetur da Najeriya ke shigo dashi daga kasashen waje yayi kasa sosai irin wanda ba’a taba gani ba a cikin shekaru 8

Yawan man fetur din da Najeriya ke shigo dashi daga kasashwn waje yayi kasa sosai ta yanda ba’a taba ganin hakan ba a cikin shekaru 8 da suka gabata.

Wannan na da alaka da yanda matatar man fetur ta Dangote ke aiki tukuru wajan tace isashshen man fetur da kuma danne masu yunkurin shigo da man fetur din daga kasashen waje.

Rahoton jaridar Bloomberg yace daga watan Janairu na shekarar 2025 zuwa 24 ga watan yawan man fetur din da ake shigowa dashi Najeriya ya bai wuce ganga 110,000 ba a kullun.

Wannan shine mafi karancin man fetur da aka shigo dashi Najeriya daga kasashen waje idan aka kwatanta da ganga 200,000 da ake shigowa da ita kullun a shekarar 2017 inda wani lokacin har tana kaiwa ganga 400,000.

Karanta Wannan  Daga aika abokina ya gwada Budurwata yace yana sonta dan in gane ko da gaske tana sona, Yanzu in gajarce muku zance ya aureta>>Inji Usman Zannah

Rahoton yace matatar Dangote wadda ke da karfin data fi kowace matatar man fetur a Afrika da Turai tasa wasu matatun man fetur a Turai dole sun daina aiki.

Hakan na faruwane duk da yake matatar man fetur din Dangoten bata aiki yanda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *