Friday, December 5
Shadow

Mutum 1,296 aka kashe a Najeriya a watan Mayu – Rahoto

Mutum 1,296 aka kashe a Najeriya a watan Mayu – Rahoto.

Wasu sabbin alƙalumma kan matsalar tsaro a Najeriya sun nuna cewa mutum 1,296 aka kashe a watan Mayu a sassan ƙasar.

Rahoton na kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a shiyyar Afirka ta yamma da yankin Sahel ya ce an samu ƙaruwar yawan waɗanda suka mutu a watan Mayu idan aka kwatanta da Afrilu inda aka kashe mutum 1,092.

Rahoton ya kuma ce mutum 1,086 aka yi garkuwa da su a sassan Najeriya a watan Mayu inda aka samu ragi idan aka kwatanta da watan Afrilu da aka yi garkuwa da mutum 1,178.

Rahoton Beacon Security and Intelligence Limited ya nuna cewa an samu ragi na kashi kusan shida cikin dari na matsalolin tsaro a Najeriya cikin watan Mayun da ya gabata, idan aka kwatanta da yadda lamarin ya kasance a watan watan Afrilu da ya gabace shi.

Karanta Wannan  Ana ta yiwa wani Fasto dariya bayan da yace an masa Wahayin Barcelona ce zata ci Inter Milan amma hakan bai faru ba

Sai dai an sami karuwar kashi goma sha tara cikin dari na mace-macen da suka auku a sakamakon matsalar ta tsaro a cikin watan na Mayu.

Rahoton ya nuna ce ragin da aka samu bai rasa nasaba da ƙoƙarin da jami’na tsaron ƙasar ke yi na yaƙi da matsalolin tsaro a sassan ƙasar.

Jihar Zamfara ce ta fi yawan mutanen da aka kashe a watan Mayu da 332 aka fi yawan kashe mutane, sai jihohin Borno da Katsina da Kebbi da kuma Neja, a cewar Rahoton na Beacon Consulting.

Kamfanin ya ce ya tattara alƙalumman ne ta hanyar rahotannin hare-hare da kashe-kashe da ake bayarwa a kafafen yaɗa labarai da kuma rahotannin jami’an kamfanin a sassan Najeriya.

Karanta Wannan  Najeriya zata fara fitar da man fetur zuwa kasashen waje

Rahoton ya ayyana cewa Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale ta fannin tsaro a sassan kasar da dama, kasancewar ana fama da matsalar harin ƴan bindiga da wasu kungiyoyi, ciki hár da Boko Haram da ta IPOB, masu fafutukar ballewa da nufin kafa kasar Biafra.

Muhukunta a Najeriya a matakai daban-daban dai kan yi ikirarin daukar matakai don inganta tsaro, amma za a iya cewa matsalar na nan ba ta kau ba.

A hirarsa da BBC, shugaban kamfanin tsaron na Beacon Malam Kabiru Adamu ya ce ya ce akwai bukatar gwamnatoci a matakai daban-daban su fitar da tsarin da zai gaggauta rage talauci a tsakanin al.’umma, sannan a kyautata tsarin yaƙi da ta`addanci ta hanyar cusa al`umma a ciki, wato ta yadda za su dinga samar da bayanai ga jami`an tsaro da bangarorin da yaƙi da ta`addancin ya shafa.

Karanta Wannan  Kalli Karin Hotuna da Bidiyo na abinda tshageran Dhaji sukawa sojojin Najeriya da suka je ceto daliban jihar Kebbi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *