
Shugaban kungiyar ‘yan Uwa Musulmi ta Najeriya wadda aka fi sani da shi’a, Ibrahim Zakzaky ya bayyana cewa, kasar Iran Miliyoyin kudade ta kashe wajan kaiwa kasar Israyla hare-hare.
Saidai yace ita kuma Israylan ta kashe Biliyoyi ne wajan tare wadannan hare-haren.
Ya bayyana hakanne a wani faifan Bidiyon sa da aka gani yana jawabi akan yakin da ya barke tsakanin kasar Israyla da Iran.