Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kasa Ta Umarci Kakakin Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa Da Ya Gurfana A Gabanta Bisa Batancin Da Ya Yi Wa Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa, Abdullahi Ganduje.

Babban sufeton ƴansanda na ƙasa Kayode Egbetokun, ya umurci rundunar bincike ta kwamitin kula da ayyukan ƴan sanda ta kawo Sanusi Bature Dawakin-Tofa, mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf, zuwa hedikwatar ƴansanda ta ƙasa domin amsa tuhumar ɓatanci da ake yi masa akan dakatar da shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar sa.
A shekarar 2024, kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC a mazaɓar Ganduje ya dakatar da Ganduje daga jam’iyyar, bisa zargin cin amanar jam’iyya da kuma rashin biyan kuɗin membobinsu.
A wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 23 ga Mayu, 2025, da lamba CR/3000/IGP-SEC/MU/ADM/14/ABJ/VOL 118/57, wadda aka aike wa sakataren gwamnatin jihar Kano, Sufeto janar ya buƙaci a saki Sanusi Bature Dawakin-Tofa domin bayyana a gaban SP Mojirode B. Obisiji a ranar Alhamis, 29 ga Mayu, 2025.