
Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa, cewa a zabi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ko da ba’a hada da kiran sunan Kashim Shettima ba, duk yana nufin a zabesu tarene.
Ya bayyana hakane a kafar sada zumuntarsa.
Hakan na zuwane yayin da rikici ya taso a cikin jam’iyyar inda ake zargin shugaba Tinubu ba zai ci gaba da tafiya da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa ba a zaben shekarar 2027.
A jiya dai a wajan taron nuna goyon bayan Tinubu na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga Arewa maso gabas, an baiwa hammata iska bayan cewa a zabi Tinubu ba tare da kiran sunan Kashim Shettima ba.