Friday, December 5
Shadow

‘Yan kasuwar man fetur sun kara kudin man a gidajen sayar da man fetur na Najeriya

A yayin da rikicin kasar Israyla da Falasdiynawa yasa farashin danyen man fetur a kasuwannin Duniya ya tashi zuwa dala $74 kan kowace ganga.

‘Yan kasuwar man fetur a Najeriya sun kara farashin man fetur din nasu a gidajen mai daban-daban.

Misali gidan man Aiteo ya kara farashin man fetur dinsa zuwa Naira 840 kan kowace lita daga Naira 835 da ake sayar da ita a baya.

Hakanan gidan man Pinnacle sun kara farashin man fetur dinsu zuwa 845 akan kowace lita maimakon Naira 829 da suke sayarwa a baya.

Dangote kuwa ya kara farashin man nasa ne zuwa Naira 840 kan kowacw lita maimakon 830 da yake sayarwa a baya.

Karanta Wannan  A karo na 2, Sanata Godswill Akpabio karara ya bayyana tsoron Trump yake ji yayin da 'yan Najeriya suka bukaci jin Abinda majalisar Dattijai zata ce kan Barhazhanar da Trump din yawa Najeriya

Ana tsammanin farashin man fetur din zai ci gaba da tashi a kasuwannin Duniya saboda rashin tabbas a kasuwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *