
Tsohon Kakakin majalisar Dattijai, Sanata David Mark ya bayyana cewa, Kwanannan mutane zasu daina yadda da cewa gwamnati zata karesu inda zasu fara tashi tsaye suna kare kansu.
Mark ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Paul Mumeh inda yace lamarin tsaro ya kazance.
Ya jawo hankalin gwamnati data dauki mataki ko kuma nan gaba kadan mutane zasu fara tashi tsaye suna kare kansu.
Ya bayyana hakane a yayin da aka kaiwa jiharsa ta Asali, Benue hari inda aka kashe mutane sama da 100.