
‘Yan kasuwar man fetur da yawa na ganawa bisa yunkurin Matatar Dangote na fara rarraba man fetur dinsa a fadin Najeriya da tankokinsa.
A ranar June 15 Matatar Dangote tace tana shirin kawo tankokin dakon man fetur 4000 da zasu fara jigilar man fetur din Dangoten zuwa sassa daban-daban na kasarnan daga ranar 15 ga watan Augusta me zuwa.
‘Yan kasuwar sun ce suna tattaunawa kan lamarin dan daukar matakin da ya dace.
Sun koka da cewa wannan yunkurin na Dangote zai saka ‘yan kasuwa da yawa su karye