
‘Yan majalisar wakilai biyu, Peter Akpanke, da Paul Nnamchi sun bar jam’iyyunsu inda suka koma jam’iyyar APC.
Akpanke ya fito daga jihar Cross River ne kuma an zabeshi a karkashin jam’iyyar PDP amma yanzu ya bar jam’iyyar zuwa APC.
Shi kuwa Nnamchi ya fito daga jihar Enugu ne kuma an zabeshi a karkashin jam’iyyar Labour party ne amma yanzu ya koma jam’iyyar APC.
Kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas ya sanar da komawarsu APC a yayin zaman majalisar ranar Talata.