Friday, December 5
Shadow

Gaskiya ka iya Karya, ta ya zaka ce mana kun kammala jami’a da dan shekaru 13?>>Atiku Abubakar ya caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, akwai daure kai da rainin hankali ace wai Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kammala jami’a tare da dan shekaru 13.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a yayin da yake kaddamar da shirinsa na Renew Hope Agenda a Abuja ya bayyana wani me suna Alex Zingman  da cewa, abokin karatunsa ne.

Saidai Atiku yace shi wannan me suna Alex Zingman da Tinubu yace sun kammala jami’ar Chicago State University (CSU) tare a shekarar 1979, an haifeshine a shekarar 1966, watau yana da shekaru 13 kenan suka kammala karatu tare da shugaba Tinubu.

Karanta Wannan  Matashi daga Kano, Ibrahim Bala ya kirkiro na'urar da zata taimaka wajan hana direbobi Hadari

Dan haka Atiku a sanarwar da ya fitar ta hannun me magana da yawunsa, Paul Ibe yace wata kila kundin tarihin Duniya ya manta ne bai saka wannan abokin karatu na Tinubu a cikin kundin ba bisa lura da cewa shine zai kasance dalibi mafi karancin shekaru da ya kammala karatun Jami’a.

Atiku yace haka Tinubu yace mana ya kammala makarantar Government College, Lagos amma kuma har yanzu babu wani da ya fito yace sun yi karatu tare.

Atiku yace kuma shi wannan mutumin da Tinubu ke cewa sun yi karatu tare ana zarginsa da aikata miyagun laifuka ciki hadda zargin safarar makamai.

Karanta Wannan  Ya kamata 'yan Najeriya su rima godewa kokarin da muke domin ita matsalar tsaro ba'a magance ta a rana daya>>Inji Me baiwa shugaban kasa shawara kan matsalar tsaro, Nuhu Ribadu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *