Friday, December 5
Shadow

Sai Tinubu ya yi sa’a ma zai zo na uku a zaɓen 2027— In ji El-Rufai

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ba ya damu da yawan sauya sheƙa da ake yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

A wata hira da aka yi da shi kai tsaye a shirin Arise TV a daren Litinin, El-Rufai ya ce shugaban ƙasa mai ci yana ɗaukar matsayin cewa tuni an gama da dawowar sa karo na biyu, ganin yadda wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa ke sauya sheƙa zuwa APC.

Sai dai ya bayyana cewa: “Tinubu ba zai ci zaɓe ba. A gaskiya, zai yi sa’a idan ma ya zo na uku.”

Tsohon gwamnan ya zargi gwamnatin Tinubu da halin ko in kula dangane da matsanancin halin tsaro da ƙasar ke ciki, yana mai bayyana cewa an cire naira biliyan 100 daga Asusun Tarayya cikin watanni 15 da suka gabata ba tare da amincewar jihohi ko majalisar dokoki ba.

Karanta Wannan  Bayan kammala karatu na tsawon shekaru 5 yanzu na shirya aure>>Inji Wannan matashiyar

Ya ce: “Tun cikin watanni 15 da suka wuce, ana cire biliyan 100 daga Asusun Tarayya ana tura wa hukumomin tsaro. Amma me ya sauya? A shekarar 2024, an sace sama da mutane miliyan 2.2, an kashe mutum 615,000. Nigeria na cikin yaƙi ne? Wannan adadi ya fi na shekaru 8 na Buhari muni. Kuma duk wannan ƙididdiga daga Hukumar Kididdiga ta Ƙasa ce, ba ta wani waje ba. Wannan kuɗi ne da aka ɗauka daga Asusun Tarayya ba tare da amincewar Majalisar Tarayya ba. Wannan saba doka ne, kuma abin a tsige shugaban ƙasa ne, amma har yanzu ana cigaba da hakan. Ina wannan naira tiriliyan 1.5 ta tafi? Me ya sa matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara? Me ya sa gwamnati ke buƙatar al’umma su kare kansu?”

Karanta Wannan  Albashin sanatocin Najeriya su 109 zai iya biyan Albashin Farfesoshi 4,708, Kowane sanata yana karbar Naira Miliyan 21.6 duk wata, yayin da kowane Farfesa kuma ke karbar Naira 500,000 duk wata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *