
Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Malika kenan ko ace Amarya a wadannan Bidiyon inda ta dauki hankula sosai bayan da aka ganta ta sha kwalliya irin ta amare.
Malika wadda abokin aikinta, Abdul M. Shareef zai aura an ganta a Bidiyon tare da kawayenta suna taka rawa.
Da yawa dai sun ce ta yi kyau.