
Wani jigo a jam’iyyar APC ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar kada ya nemi sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027.
Eze Chukwuemeka Eze daga jihar Rivers ya yabawa El-Rufai da Amaechi da Atiku da sauransu da suka hada kai dan kafa sabuwar jam’iyya me suna ADA dan su kayar da Tinubu a zaben shekarar 2027.
Yace Tinubu bai yiwa ‘yan Najeriya wani aikin a zo a gani ba a shekaru 2 da yayi yana mulkar Najeriya inda yace dan haka ya kamata ya hakura kar ya sake tsayawa takarar shugaban kasa.