
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa yana matukar yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu biyayya.
Yace duk abinda yasa shi ya aikata zai aikata dari bisa dari.
Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gyara barakar siyasa ta cikin gida data kunno kai a jihar Kano kuma ya taimaka masa wajan zama mataimakin kakakin majalisar Dattijai.
Ya bayyana hakane game da wata kungiya data ce tana son shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya daukeshi a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2027.
Jibrin yace bai san wannan kungiyar ba amma yana godiya da nagartarsa da suka duba.
Yace kuma a bar maganar yanzu saboda yanzu lokacin mulki ne ba lokacin siyasa ba.