Friday, December 5
Shadow

Ni da kaina na je ofishin EFCC ba kama ni akai ba>> Inji Tsohon Me kula da kudi na kamfanin mai na kasa, NNPCL, Umar Ajiya Isa da ake zargi da satar Dala Biliyan $7.2 na gyaran matatun man fetur din Najeriya

Tsohon Babban Jami’in Kudi (CFO) na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Umar Ajiya Isa, ya karyata rahotannin da ke cewa jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kama shi a ranar Litinin bisa zargin almundahana.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ajiya ya bayyana cewa, akasin yadda ake yadawa, shi da kansa ne ya je ofishin EFCC domin amsa tambayoyi, ba tare da an kama shi ba dangane da zargin handame cinikin man fetur har ma dala biliyan $7.2 a matatun mai na Warri da Port Harcourt.

“Ba wanda ya kama ni kan zargin batan wata dala biliyan $7.2 a matatar mai. Na je ofishin EFCC ne da kaina domin amsa tambayoyi sannan na koma gida. Na ji takaici ganin rahotanni a kafafen yada labarai da ke cewa an kama ni bisa zargin damfara,” in ji shi.

Karanta Wannan  An kama matashi me suna Haruna yawa yarinya me shekaru 3 fyàdè a ranar 1 ga Ramadana

“Na yi aiki a NNPC Limited kuma na baro wurin da mutuncina kuma na yi aiki na cikin tsabta. Babu wanda ya taba zargina da wani nau’in damfara duka tsawon lokacin da na yi a kamfanin. Wadanda ke yada wannan ƙarya suna so ne kawai su bata mini suna.”

Isa ya ce a shirye ya ke a kowane lokaci ya kare mutuncinsa da shekaru da ya kwashe yana aiki a NNPCL.

“Ina nan cikin ƙasar nan kuma a duk lokacin da EFCC ta bukaci na bayyana a gaban ta, zan je ba tare da wata matsala ba,” in ki Ajiya.

A makon da ya gabata ne dai Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kuɗaɗen Al’umma karkashin jagorancin Sanata Aliyu Wadada, ya bayyana cewa akwai zargin sama-da-faɗi da wasu Kuɗaɗe da suka kai tiriliyoyin Naira a cikin bayanan kudi da aka tantance na NNPCL.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Tinubu ya ɗage tafiyar sa don Alhinin Daliban jihar Kebbi

Kwamitin ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa da takaici.

Kwamitin ya ce damuwar na da nasaba ne da bayanan kudi na NNPCL da aka tantance daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Nan take kwamitin ya mika jerin tambayoyi 11 ga sashen kudi na NNPCL tare da ba su mako guda su dawo da amsoshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *