
Tauraron dan kwallon Portugal, Cristiano Ronaldo ya sabunta kwantirakinsa da kungiyar Al Nasr ta kasar Saudiyya.
Daga cikin damarmakin da aka bashi shine yana da bakin magana akan duk dan wasan da kungiyar zata siya.
Ronaldo dan shekaru 40 ya amince da ci gaba da zama a kungiyar ta Al Nasr har zuwa shekarar 2027.
Tun a shekarar 2023 ne dai Ronaldo ya je kungiyar ta Al Nasr.