
Wata mata me shekaru 46 da bata taba aure ba ta koka da cewa maza na gudunta suna cewa ta tsufa.
Tace yawanci mazan dake zuwa wajanta mazan aurene kuma ba aure ke kaisu wajanta ba, suna nemanta da lalata ne.
Tace da yawa idan suka ganta sai su ce ta tsufa.
Ta koka da cewa ba ita kadai bace a wajan mahaifiyarta ba amma ita kadai ce bata yi aure ba.
Matar tace wallahi bata taba sanin Namiji ba, kuma idan mutum na da yanda zai gwada, yana iya gwadawa ya gani.
Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita a wani gidan rediyo me suna Agidigbo FM inda tace tana neman taimakon a samo mata mijin aure.