
A yaune shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanyawa dokar canja fasalin Haraji hannu.
Shugaban ya sakawa dokar hannu a fadarsa wanda lamarin ya samu halartar kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio da takwaransa na majalisar wakilai, Tajudeen Abbas da wasu gwamnoni da sauran manyan ma’aikatan Gwamnati.
Sabuwar dokar harajin dai a cewar shugaban zata kawo ci gaba sosai a kasarnan har ga wadanda ba’a haifa ba.

