
Hukumar zabe me zaman kanta tace zata ci gaba da rijistar masu zabe a ranar 17 ga watan Yuli a jihar Anambra inda kuma za’a ci gaba da yi a gaba dayan Najeriya a ranar 18 ga watan Augusta.
Shugaban hukumar, Prof. Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da aka yi ranar Alhamis a Abuja.
Ya bayyana cewa, za’a fara rijistar ne a jihar Anambra saboda zaben gwamna da za’a gudanar a jihar.