
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta fara aiwatar da sababbin dokokin haraji da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu ba sai a watan Janairun 2026.
Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan bikin saka wa dokokin huɗu hannu a yau Laraba, shugaban kwamatinn hukumar tattara harajin Zach Adedeji ya ce za su kammala tsara komai kafin lokacin aiwatar da su.
Ya ƙara da cewa za su yi amfani da tazarar wata shidan wajen bai wa waɗanda ke da alhakin aiwatar da dokar damar shiryawa da kuma tabbatar da cewa an wayar da kan dukkan ‘yan Najeriya game da dokokin.
Ya tabbatar da cewa saka wa dokokin hannu ya sauya sunan ma’aikatarsa daga Federal Inland Revenue Service (FIRS) zuwa Nigeria Revenue Service.