Friday, December 5
Shadow

Najeriya ce ta daya wajan yawan mutanen da basu samun wutar lantarki a Duniya>>Inji Bankin Duniya

A sabon rahoton sa na shekarar 2025, bankin Duniya ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya Miliyan 86.8 ne ke cikin duhu basa samun wutar Lantarki a Najeriya.

Bankin yace wannan shine mutane mafiya yawa da ya zarta na kowace kasar Duniya.

Rahoton yace a cikin kasashen 20 da basa samun ingantacciyar wutar lantarki, guda 18 na Afrika ne.

Rahoton yace kaso 60 cikin 100 na ‘yan Najeriya ne ke samun wutar lantarki sannan kaso 26 cikin 100 na ‘yan kasar ne ke amfani da makamashi me tsafta na girki.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Adam A. Zango ya ke cin Angonci da amaryarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *