Friday, December 5
Shadow

Shugaban ‘yansandan Najeriya ya bayar da umarnin yin bincike kan zargin biyan dansanda Naira Miliyan 2 a matsayin kudin ritaya

Shugaban ‘yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin yin bincike dan gano gaskiyar ikirarin wani tsohon dansanda da yace an biyashi Naira Miliyan 2 a matsayin kudin sallama.

Hutudole ya ruwaito muku cewa, Bidiyon dansansan ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda ya jawo cece-kuce.

Dansandan wanda yayi ritaya da mukamin Superintendent of Police yace ba zai karbi Naira Miliyan 2 ba saboda ta masa kadan bayan shafe shekaru 35 yana aiki a matsayin dansanda.

Dansandan wanda yayi ritaya a watan October 1, 2023 yace hukumar kula da fansho na ‘yansanda ta sanar dashi cewa kudin sallamarsa Naira Miliyan 2 ne sannan akwai Naira Miliyan daya ta bashin kudin fansho da yake bi.

Karanta Wannan  Ko ta bar Musulunci ne? Wani ya tambaya bayan ganin wadannan hotunan na Tauraruwar fina-finan Hausa, A'isha Saleh

Kakakin ‘yansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa, shugaban ‘yansandan ya bayar da umarnin yin bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *