
Daga yanzu zuwa kowanne lokaci, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, zai mika takardar murabus dinsa, in dai ba canja ra’ayi ya yi ba.
Majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa za a maye gurbin Ganduje da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na ƙasa na yanzu har zuwa lokacin babban taron jam’iyyar da za a yi a watan Disamba.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na murabus na da nufin shawo kan korafe-korafe daga jiga-jigan jam’iyyar daga yankin Arewa ta Tsakiya, da kuma ƙara karfin tasirin muryar adawa daga cikin jam’iyyar da ke ƙara ta’azzara.
Idan za a iya tunawa an nada Ganduje a watan Agusta 2023 bayan murabus din Abdullahi Adamu daga wannan mukami.
Tun daga lokacin, jiga-jigan siyasa daga Arewa ta Tsakiya suna ci gaba da neman a mayar da kujerar shugabancin jam’iyyar ga yankinsu.
Majiyoyi sun bayyana cewa Ganduje, wanda ya fito daga Kano, an shawarce shi da ya sauka daga kujerar ne domin bai wa jam’iyyar damar tsara dabaru gabanin zaben 2027.