
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC a yau, Juma’a.
Ya bayyana hakane a wata wasika da ya aikewa jam’iyyar. A cikin wasikar, Ganduje ya bayyana dalilin rashin lafiya a matsayin abinda yasa ya sauka daga mukamin nasa.
Tsohon Gwamnan jihar Kanon ya sha suka daga mutanen yankin Arewa maso gabas saboda zargin rashin goyon bayan Kashim Shettima a matsayin abokin takarar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa.
An bayyana cewa wani daga cikin mataimakan Gandujenne zai zama shugaban riko na jam’iyyar kamin babban zabenta a watan Disamba me zuwa.