Friday, December 5
Shadow

Bani da lafiya a taimaka a barni in je neman magani kasar waje>>Yahya Bello ya roki kotu a yayin da ake shari’a kan zargin satar Naira Biliyan 80.2 da ake masa

Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya roki babbar kotun dake da zama a Abuja data taimaka ta barshi ya je kasar waje neman magani.

Yahya Bello ya roki kotun data bashi fasfonsa wanda a baya ya bayar dan cika sharadin bayar da belinsa.

Bello ya mika wannan korafinne ta hannun lauyansa, Joseph Daudu (SAN),

Ana shari’a ne kan zargin da akewa Tsohon gwamnan na satar Naira Biliyan 80.2 wanda hukumar EFCC ta shigar da kararsa.

Karanta Wannan  Maganar Wike ya baiwa 'ya'yansa manyan filaye a Abuja: Atiku ne saboda kiyayya yake son batamin suna>>Inji Wike

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *