
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Gwamnatinsa ta ‘yan Najeriya ce kuma ayyukansa dan ci gaban Najeriya ne.
Shugaban ya bayyana hakane ranar Juma’a a wajan kaddamar da wani titi daya gina a Abuja da ya hada Kabusa da Ketti.
Shugaban yace yana nan kan bakansa na samarwa ‘yan Najeriya da makamashi, Tituna, makarantu da Asibitoci.