Friday, December 5
Shadow

Ya kamata ka mayar da hankali wajan yaki da talauci>>Gwamnonin APC suka gayawa shugaba Tinubu

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Gwamnonin jam’iyyar APC sun baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar mayar da hankali wajan yaki da Talauci.

Sun bayyana hakane a wata sanarwa da suka fitar ta bayan taron da suka yi a garin Benin City na jihar Edo.

Shugaban kungiyar gwamnonin ta APC, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ne ya bayyana hakan a jawabin da ya karanto.

Gwamnonin sun goyi bayan tayar da komadar tattalin arziki da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke yi bisa hadin gwiwarsu.

Gwamnonin sun bayyana jin dadin hadakar aiki da ake samu tsakaninsu da gwamnatin tarayya inda suka ce ana samun ci gaba.

Saidai sun ce ya kamata a fadada zuba jari a bangaren samar da abinci, samar da ayyukan yi, da kawar da talauci da karfafa masu kananan masana’anu, da bayar da tallafi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Kalaman da Sheikh Lawal Triumph ya fadi akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Sam basu dace ba, kuma nasan zaku ce ni dan fim ne be kamata in saka baki ba, to Ku sani Annabu aka taba>>Inji Bosho

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *