Friday, December 5
Shadow

Wata Sabuwa: Ashe Ashe Daloline ake zargin Ganduje ya karba ya tafka magudin zabe shiyasa Tinubu ya tursasa masa sauka, ji cikakken labarin

Bayan da shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ajiye mukaminsa da kuma bayyana cewa zai kula da lafiyarsa ne.

Bayanai na ci gaba da fitowa kan ainahin dalilin da yasa ya sauka daga mukamin nasa.

Rahoton majiyarmu yace Ganduje ya Zaben babban birnin tarayya, Abuja da aka yi, an zargi Ganduje da karbar kudi ya baiwa wanda yafi bayar da kudi takarar zabe.

Rahoton yace bayan kammala zaben ne wasu suka shigar da korafi inda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yasa a yi bincike.

Bayan gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sakamakon binciken ne sai ya kira taron kungiyar Gwamnonin APC inda ya shaida musu halin da ake ciki.

Karanta Wannan  Ya Bude Shagon Siyar Da Yajin Daddawa Bayan Ya Kammala Digiri A Jami'ar Bayero

Sannan aka nada wasu wakilai daga cikin gwamnonin ciki hadda Mai Mala Buni suka samu Ganduje suka gaya masa ya sauka girma da arziki ko a saukeshi kuma a bincikeshi game da zargin rashawa da cin hanci.

Saidai duk da haka, Ganduje ya ki sauka daga kujerar tasa inda yayi ta kokarin ganin shugaban kasar dan ya rokeshi ya barshi akan kujerar shugaban APC har zuwa watan Disamba da za’a gudanar da babban zaben jam’iyyar.

Saidai hakan ya ci tura, an sake turawa Ganduje shugaban hukumar ‘yansandan farin kaya, DSS inda yace masa ya sauka daga kan kujerar shugabancin APC inda anan dole ya sauka ba dan yana so ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Amarya ta dauki hankula saboda yin karatu a wajan Bikinta

A baya dai shugaba Tinubu yayi yunkurin sauke Ganduje daga shugabancin APC amma hakan bata samu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *