Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: A karshe dai Hukumomin Saudiyya sun amince a binne gawar marigayi, Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina.

Mustapha ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta cewa, “Alhamdulillah an samu amincewar (hukumomi), za a ɗauki Aminu Alhassan Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa Madina. Za a yi jana’iza gobe da safe in sha Allah.”

A safiyar jiya Asabar ne da attajirin ɗankasuwar ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, amma iyalansa suka jinkirta binne shi domin a cewarsu, suna su ne su cika masa burinsa na kasancewar a binne a garin na Madina.

An dai gudanar masa da sallar da gawa ba ta kusa a jihar Kano, wanda Sheikh Ibrahim Khalil ya jagoranta.

Karanta Wannan  Da Duminsa:Kalli Bidiyon yanda wani dake tsaye a bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ya ke jiki ya Fhadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *