
Kwamandan Runduna ta 17 na Sojojin Najeriya da ke Katsina, Birgediya Janar Babatunde Omopariola, ya umarci dakarunsa da su kama kuma su kai rahoto kan duk wani soja da aka kama yana shan wiwi ko amfani da miyagun kwayoyi.
Janar Omopariola ya bayar da wannan umarni ne a ranar Asabar a garin Katsina, yayin bikin ranar Sojojin Najeriya ta shekarar 2025 (NADCEL), wanda aka gudanar a ofishin rundunar.
A cewarsa, shan miyagun kwayoyi na rage karfin ma’aikata a Najeriya kuma yana barazana ga makomar kasa.
Ya gargadi jami’ai da dakarun rundunar da su guji amfani da kwayoyi haramtattu, musamman a cikin bariki.
Kwamandan ya bayyana amfani da miyagun kwayoyi a matsayin wani babban abin da ke lalata ginshikin zamantakewa da lafiyar al’umma a Najeriya.