
Major General Ijioma Nwokoro Ijioma ya bayyana cewa, babu dan ta’addar da ya fi karfin sojojin Najeriya.
Janar din me ritaya na daga cikin wadanda aka tura zuwa kasar Sudan dan kwantar da tarzoma a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015.
Hakanan ya yaki kungiyar Bòkò Hàràm inda ya kwato karamar hukumar dake hannunsu.
Janardin wanda akawa ritayar dole ya bayyana cewa matsalar Najeriya shugabanci ne kuma shiyasa shuwagabannin saboda sun san basu da nagarta sai su rika amfani da kabilanci da addini wajan neman nasarr cin zabe.