
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya talauce bashi da kudi.
Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Garba Shehu inda ya kara da cewa kuma ya sauka daga mulki da mutuncinsa saboda bai karbi cin hanci daga girin kowa ba.
Garba Shehu ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai a yayin da yake kaddamar da wani littafi kan irin abinda ya fuskanta lokacin yana aiki da shugaban kasa.
Garba yace dalilin da yasa shugaba Buhari baya hira da ‘yan jaridu shine yana son aikinsa ne ya rika amfanar da mutane.