
‘Yan Adawa da suka hada kai cikin jam’iyyar ADC sun yi taro na musamman inda suka tabbatar da yin aiki tare dan kayar da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa.
Atiku Abubakar ya wallafa hotunan taron nasu wanda aka ga Nasir El-Rufai a ciki da kuma Peter Obi da David Mark da sauransu.


