
Tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Asase ya bayyana cewa, au yaran Rarara sun kai 400 kuma kowanne ya bashi gida da mota.
Ya bayyana hakane bayan da Nazir Ahmad Sarkin Waka ya wallafa hoton Bidiyon sabuwar motar da ya siya wadda yace dan ya hucewa Masoyansa haushin gorin da aka rika musu ne.
Nazir dai duk da bai kira suna ba amma da yawa sun yi amannar cewa da Rarara yake inda yace motarsa zata sayi ta Rarara 3 hadda canji.
Saidai Tijjani Asase yace ba gasar mota suke bukata ba, ayyukan Alheri na Rarara ya kamata Nazir Ahmad Sarkin Waka ya rika gasa dasu ba wai mota ba.
Ya bayar da misalin Abdul Amart Maikwashewa inda yace irin gasar da yake da Rarara wajan taimakon mutane irintace ake son a rika yi.