Monday, December 16
Shadow

Babbar Sallah: ‘Yan Najeriya na kokawa kan tsadar dabbobi

Babbar Sallah: ‘Yan Najeriya na kokawa kan tsadar dabbobi.

Yayin da babbar sallah ke ƙara ƙaratowa ‘yan Najeriya na kokawa dangane da tsadar dabbobi musamman raguna waɗanda su ne aka fi amfani da su a lokacin layya.

Wasu masu sayar da raguna da wakilin BBC a Legas ya tattauna da su sun ce farashin raguna ya ninka sau uku daga yadda aka sani a bara.

“Ragon da aka saya a bara naira dubu 100 yanzu ya zama naira dubu 300. Haka shi ma na naira dubu ɗari biyu yanzu ya zama naira ɗari biyar”. In ji wani mai sayarwa.

Su ma masu sayen dabbobin da dama da aka tattauna da su sun ce bai zama lallai su yi layyar ba duk da dai wasu sun ce “amfani kuɗi shi ne a kashe su ta hanyar da ta dace.”

Karanta Wannan  Matatar Dangote ta ɗage fara samar da fetur a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *