Friday, December 5
Shadow

Ko Tinubu danshi zai nada shugaban INEC, sannan ya ba matarshi mukamin Shugabar Alkalan Najeriya, sai ya fadi zabe a 2027>>Solomon Dalung

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Tsohon Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya bayyana cewa, ko wane irin shiri gwamnatin Tinubu zata yi a zabe me zuwa, sai ta fadi zaben shekarar 2027.

Dalung ya bayyana hakane a ganawarsa da manema labarai na kafar News Central dake Jos.

Dalung yace, Tinubu ko dansa zai baiwa shugaban hukumar zabe me zaman kanta, INEC, sai ya fadi zabe a shekarar 2027. Hakanan ko matarsa zai baiwa shugabar Alkalan Najeriya sai ya fadi zabe.

Yace hakanan kuma ko da duka Gwamnonin Najeriya zasu koma jam’iyyar APC dik wannan ba zai hana Tinubu faduwa a zaben shekarar 2027 ba.

Dalung yayi kira ga ‘yan Najeriya da su dauki matakin shiri na musamman da zuwan zaben shekarar 2027.

Karanta Wannan  Rubabun 'yan siyasa ba zasu ga kokarin Tinubu ba>>Inji Wike

Yace kuma APC zata iya rushewa saboda yawanci neman mulki ne yake kai mutane cikin ta ba wani abuba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *