Friday, December 5
Shadow

Subhanallahi: Ji yanda ‘yansandan Najeriya suka kama wani limamin Masallaci na bata rayuwar karamar yarinya

Yan sanda a jihar Osun sun kama wani limamin masallaci me suna Babasanya-Araka da zargin yin lalata da karamar yarinya.

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Lamarin ya farune a garin Ede na jihar, kuma ya tayar da hankulan jama’ar garin.

Mutane sun taru suka fara dukan limamin saidai jami’an tsaro sun je sun kwaceshi.

Kakakin ‘yansandan jihar, Abiodun Ojelabi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace da suka je Wajan har Amotekun sun kama limamin inda suka damka musu shi.

Yace zasu gudanar da bincike akanshi kamin su mika shi zuwa SCID.

Wani shaida yace yarinyar da ake zargin limamin da yin lalata da ita shekarunta 8 kuma ta bace ana nemanta sai gata an ganta tana kuka jini na zuba a gabanta.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu zai shiryawa 'yan kwallon kwando mata da suka ciyo kofin kwallon Kwando na mata na Afrika liyafa ta musamman, da yawa sun fara cewa akwai yiyuwar suma shugaban zai musu kyautar daloli

Yace Tuni ka kaita Asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *